1 Ya Ubangiji Allah, Mai Cetona,Duk yini ina ta kuka,Da dare kuma na zo gare ka.
2 Ka ji addu'ata,Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako!
3 Wahala mai yawa ta auko mini,Har ina gab da mutuwa.
4 Ina daidai da sauran mutanen da suke gab da mutuwa,Dukan ƙarfina ya ƙare.
5 An yashe ni a cikin matattu,Kamar waɗanda aka karkashe,Suna kuma kwance cikin kaburburansu,Waɗanda ka manta da su ɗungum,Waɗanda taimakonka ya yi musu nisa.
6 Ka jefar da ni cikin zurfin kabari,Da cikin rami mafi zurfi, mafi duhu.