7 Fushinka yana da nauyi a kaina,An turmushe ni a cikin tuƙuƙinka.
8 Ka sa abokaina su yashe ni,Ka sa sun ware ni.An kange ni, ba yadda zan kuɓuta.
9 Idanuna sun raunana saboda wahala.Ya Ubangiji, kowace rana ina kira gare ka,Ina ta da hannuwana zuwa gare ka da addu'a!
10 Kakan yi wa matattu mu'ujizai ne?Sukan tashi su yabe ka?
11 Akan yi maganar madawwamiyar ƙaunarka a kabari?Ko amincinka a inda ake hallaka?
12 Za a iya ganin mu'ujizanka a cikin duhu?Ko kuwa alherinka a lahira?
13 Ya Ubangiji, ina kira gare ka, neman taimako,Kowace safiya nakan yi addu'a gare ka.