40 Ka rurrushe garun birninsa,Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.
41 Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa,Maƙwabtansa duka suna yi masa ba'a.
42 Ka ba maƙiyansa nasara,Ka sa dukansu su yi murna.
43 Ka sa makamansa su zama marasa amfani,Ka bari a ci shi da yaƙi.
44 Ka ƙwace masa sandan sarautarsa,Ka buge gadon sarautarsa ƙasa.
45 Ka sa shi ya tsofe kafin lokacinsa,Ka rufe shi da kunya.
46 Har yaushe za ka ɓoye kanka, ya Ubangiji?Har abada ne?Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?