7 Amma Ubangiji sarki ne har abada,Ya kafa kursiyinsa domin yin shari'a.
8 Yana mulkin duniya da adalci,Yana yi wa mutane shari'a da gaskiya.
9 Ubangiji mafaka ne ga waɗanda ake zalunta,Wurin ɓuya a lokatan wahala.
10 Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji,Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba.
11 Ku yabi Ubangiji, shi da yake mulki a Sihiyona!Ku faɗa wa kowace al'umma abin da ya yi!
12 Allah yana tunawa da waɗanda suke shan wuya,Ba ya mantawa da kukansu,Yana kuma hukunta waɗanda suke cutarsu.
13 Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai!Ka dubi irin wulakancin da maƙiya suka yi mini!Ka kuɓutar da ni daga mutuwa, ya Ubangiji,