4 A gare ka shekara dubu, kamar kwana ɗaya ne,Kamar jiya ce wadda ta shige,Gajeruwa ce kamar sa'a guda ta dare.
5 Kakan kwashe mutane kamar yadda ambaliyar ruwa take yi,Kamar mafarki suke, ba su daɗewa.Kamar tsire-tsire suke waɗanda suke tsirowa da safe,
6 Su yi girma har su yi huda,Sa'an nan su yi yaushi su bushe da yamma.
7 Mun halaka ta wurin fushinka,Mun razana saboda hasalarka.
8 Ka jera zunubanmu a gabanka,Zunubanmu na ɓoye kuwa,Ka sa su a inda za ka gan su.
9 Fushinka ya gajerta tsawon ranmu,Ranmu ya ƙare kamar ajiyar zuciya.
10 Tsawon kwanakin ranmu duka a ƙalla shekara ce saba'in,In kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne.Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaruSuke kawo mana, damuwa ce da wahala,Nan da nan sukan wuce,Tamu da ƙare.