1 Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya,A raira waƙa don girmansa, Allah mafi ɗaukaka,
2 A yi shelar madawwamiyar ƙaunarka kowace safiya,Amincinka kuma kowane maraice,
3 Da abubuwan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya,Da amon garaya mai daɗi.
4 Ya Ubangiji,Ayyukanka masu iko suna sa ni murna,Saboda abin da ka aikataIna raira waƙa domin farin ciki.
5 Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji!Tunaninka da zurfi suke!