2 A yi shelar madawwamiyar ƙaunarka kowace safiya,Amincinka kuma kowane maraice,
3 Da abubuwan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya,Da amon garaya mai daɗi.
4 Ya Ubangiji,Ayyukanka masu iko suna sa ni murna,Saboda abin da ka aikataIna raira waƙa domin farin ciki.
5 Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji!Tunaninka da zurfi suke!
6 Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba,Dakiki kuma ba zai iya ganewa ba,
7 Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire,Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta,Duk da haka za a hallaka su ɗungum.
8 Gama kai, ya Ubangiji,Maɗaukaki ne har abada.