5 Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji!Tunaninka da zurfi suke!
6 Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba,Dakiki kuma ba zai iya ganewa ba,
7 Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire,Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta,Duk da haka za a hallaka su ɗungum.
8 Gama kai, ya Ubangiji,Maɗaukaki ne har abada.
9 Mun sani maƙiyanka za su mutu,Dukan mugaye kuwa za a yi nasara da su.
10 Ka sa ni na yi ƙarfi kamar bijimi mai faɗa,Ka sa mini albarka da farin ciki.
11 Na ga fāɗuwar maƙiyana,Na ji kukan mugaye.