4 Ku raira waƙa ta farin ciki ga Ubangiji.Dukanku waɗanda suke a duniya,Ku yabe shi da waƙoƙi, kuna ta da murya da ƙarfi,Saboda farin ciki!
5 Ku raira yabbai ga Ubangiji da garayu,Ku kaɗa garayu!
6 Ku busa kakaki da ƙahoni,Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, Sarki!
7 Ki yi ruri, ya ke teku,Ke da dukan masu rai waɗanda suke cikinki,Ki raira waƙa, ke duniya,Da dukan waɗanda suke zaune cikinki!
8 Ku yi tāfi, ya ku tekuna,Ku raira waƙa tare, ya ku tuddai, don farin ciki.
9 A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya yi mulki bisa duniya!Zai yi mulki bisa dukan jama'ar duniya da adalci da gaskiya.