23 Sa'an nan mutane sukan fita su yi aikinsu,Su yi ta aiki har maraice ya yi.
24 Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa!Da hikima ƙwarai ka halicce su!Duniya cike take da talikanka.
25 Ga babbar teku mai fāɗi,Inda talikai da ba su ƙidayuwa suke zaune,Manya da ƙanana gaba ɗaya.
26 Jiragen ruwa suna tafiya a kansa,Dodon ruwa wanda ka halitta, a ciki yake wasa.
27 Dukansu a gare ka suke dogara,Don ka ba su abinci sa'ad da suke bukata.
28 Ka ba su, sun ci,Ka tanada musu abinci, sun ƙoshi.
29 Sa'ad da ka rabu da su sukan tsorata,In ka zare numfashin da ka ba su, sai su mutu,Su koma turɓaya, da ma da ita aka yi su.