39 Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu,Suka zama marasa aminci ga Allah.
40 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da jama'arsa,Ransa bai ji daɗinsu ba.
41 Sai ya bar su ƙarƙashin ikon arna,Abokan gābansu suka mallake su.
42 Abokan gābansu suka zalunce su,Suka tilasta su, su yi musu biyayya.
43 Sau da yawa Ubangiji yakan ceci jama'arsa,Amma sun fi so su yi masa tawaye,Suna ta nutsawa can cikin zunubi.
44 Duk da haka Ubangiji ya ji su sa'ad da suka yi kira gare shi,Ya kula da wahalarsu.
45 Saboda su ne ya tuna da alkawarinsa,Ya sāke ra'ayinsa saboda ƙaunarsa mai yawa.