8 Amma duk da haka ya cece su, kamar yadda ya alkawarta,Domin ya nuna ikonsa mai girma.
9 Ya tsauta wa Bahar Maliya, ta ƙafe,Har ya bi da jama'arsa su hayeKamar a bisa busasshiyar ƙasa.
10 Ya cece su daga maƙiyansu,Ya ƙwato su daga wurin abokan gābansu.
11 Ruwa ya cinye maƙiyansu,Ba wanda ya tsira.
12 Sa'an nan jama'arsa suka gaskata alkawarinsa,Suka raira yabo gare shi.
13 Amma nan da nan, suka manta da abin da ya yi,Suka aikata, ba su jira shawararsa ba.
14 Suka cika da sha'awa cikin hamada,Suka jarraba Allah,