1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Mai farin ciki ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,Mai farin ciki ne shi wanda yake jin daɗin yin biyayya da umarnansa.
2 'Ya'yansa za su zama manyan ƙasar,Zuriyar mutumin kirki za ta yi albarka.
3 Iyalinsa za su zama attajirai masu dukiya,Adalcinsa zai tabbata har abada.
4 Haske yakan haskaka wa mutanen kirki a cikin duhu,Da waɗanda suke yin alheri, da jinƙai, da gaskiya.
5 Mai farin ciki ne mutumin da yakan ba da rance hannu sake,Wato wanda yake yin harkarsa da gaskiya.
6 Mutumin kirki ba zai kāsa ba daɗai,Ba za a taɓa mantawa da shi ba.
7 Ba ya tsoron jin mugun labari,Bangaskiyarsa tana da ƙarfi,Ga Ubangiji yake dogara.