1 Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba,Aikin magina banza ne.Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba,Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.
2 Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci,A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya,Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.
3 'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji,Albarka ce ta musamman.
4 'Ya'ya maza da mutum ya haifa a lokacin ƙuruciyarsaKamar kibau suke a hannun mayaƙi.