5 Na tuna kwanakin baya,Na tuna da dukan abin da ka yi,Na tuna da dukan ayyukanka.
6 Na ɗaga hannuwana sama, ina addu'a gare ka,Kamar busasshiyar ƙasa, raina yana jin ƙishinka.
7 Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji!Na fid da zuciya duka!Kada ka ɓuya mini,Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira.
8 A gare ka nake dogara,Da safe ka tuna mini da madawwamiyar ƙaunarka.Addu'ata ta hau zuwa gare ka,Ka nuna mini hanyar da zan bi.
9 Na tafi wurinka don ka kiyaye ni, ya Ubangiji,Ka cece ni daga maƙiyana.
10 Kai ne Allahna,Ka koya mini in aikata nufinka.Ka sa in sami alherin Ruhunka.Ka bi da ni a hanyar lafiya.
11 Ka cece ni, ya Ubangiji, kamar yadda ka alkawarta.Saboda alherinka ka tsamo ni daga wahalaina!