6 Na ɗaga hannuwana sama, ina addu'a gare ka,Kamar busasshiyar ƙasa, raina yana jin ƙishinka.
7 Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji!Na fid da zuciya duka!Kada ka ɓuya mini,Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira.
8 A gare ka nake dogara,Da safe ka tuna mini da madawwamiyar ƙaunarka.Addu'ata ta hau zuwa gare ka,Ka nuna mini hanyar da zan bi.
9 Na tafi wurinka don ka kiyaye ni, ya Ubangiji,Ka cece ni daga maƙiyana.
10 Kai ne Allahna,Ka koya mini in aikata nufinka.Ka sa in sami alherin Ruhunka.Ka bi da ni a hanyar lafiya.
11 Ka cece ni, ya Ubangiji, kamar yadda ka alkawarta.Saboda alherinka ka tsamo ni daga wahalaina!
12 Saboda ƙaunar da kake yi mini,Ka kashe maƙiyana.Ka hallakar da dukan waɗanda suke zaluntata.Gama ni bawanka ne.