1 Ina ƙaunarka ƙwarai, ya Ubangiji!Kai ne mai kāre ni.
2 Ubangiji ne Mai Cetona,Shi ne garkuwata mai ƙarfi.Allahna, shi ne yake kiyaye ni,Lafiya nake sa'ad da nake tare da shi,Yana kiyaye ni kamar garkuwa,Yana kāre ni, ya ba ni lafiya.
3 Na yi kira ga Ubangiji,Yakan cece ni daga magabtana,Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
4 Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,Halaka ta auko mini a kai a kai.
5 Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
6 A shan wahalata na kira ga Ubangiji,Na yi kira ga Allahna domin neman taimako.A Haikalinsa ya ji muryata,Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
7 Sai duniya ta raurawa ta girgiza,Harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgizaSaboda Allah ya husata!