46 Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai kāre ni!Allah ne, Mai Cetona! A yi shelar girmansa!
47 Yakan ba ni nasara a kan magabtana,Yakan sa jama'a a ƙarƙashina,
48 Yakan cece ni daga maƙiyana.Ka ba ni nasara a kan magabtana, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni daga mutane masu kama-karya,
49 Don haka zan yabe ka a cikin al'ummai,Zan raira maka yabo.
50 Kullayaumi Allah yakan ba sarkin da ya naɗa babbar nasara.Yakan nuna madawwamiyar ƙauna ga wanda ya zaɓa,Wato Dawuda da zuriyarsa har abada.