1 Ina kira gare ka, ya Ubangiji mai kāre ni,Ka ji kukana!In kuwa ba ka amsa mini ba,Zan zama ɗaya daga cikin waɗanda suka gangara zuwa lahira.
2 Ka ji ni lokacin da na yi kuka gare ka neman taimako,Ina ɗaga hannuwana wajen tsattsarkan Haikalinka.
3 Kada ka kāshe ni tare da mugaye,Tare da masu aikata mugunta,Mutane waɗanda maganarsu kamar ta zumunci ce,Amma zukatansu cike suke da ƙiyayya.
4 Ka hukunta su saboda abin da suka aikata.Ka hukunta su saboda dukan ayyukansu,Ka ba su abin da ya cancance su!
5 Ba su kula da abin da Ubangiji ya yi ba,Ko kuma abin da ya halitta,Don haka zai hukunta su, ya hallaka su har abada.