1 Ina yabonka, ya Ubangiji saboda ka cece ni,Ka kuwa hana magabtana su haɗiye ni.
2 Na roƙi taimako a gare ka, ya Ubangiji Allahna,Ka kuwa warƙar da ni.
3 Ka dawo da ni daga lahira.Na gangara tare da waɗanda suke gangarawa cikin zurfafa a ƙasa,Amma ka ceci raina.
4 Ku raira yabo ga Ubangiji,Ku amintattun jama'arsa!Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya aikata,Ku yi masa godiya!
5 Fushinsa ba ya daɗewa,Alherinsa kuwa har matuƙa ne.Mai yiwuwa ne yă zama ana kuka da dare,Amma a yi murna da safe.