4 Ku raira yabo ga Ubangiji,Ku amintattun jama'arsa!Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya aikata,Ku yi masa godiya!
5 Fushinsa ba ya daɗewa,Alherinsa kuwa har matuƙa ne.Mai yiwuwa ne yă zama ana kuka da dare,Amma a yi murna da safe.
6 Ina zaune jalisan, na ce wa kaina,“Faufau ba za a taɓa cin nasara a kaina ba.”
7 Kana yi mini alheri, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni kamar a kagarar dutse.Amma sa'ad da ka ɓoye mini fuskarka,Sai in cika da tsoro.
8 Ina kira gare ka, ya Ubangiji,Ina roƙon taimakonka.
9 Wane amfani za a samu daga mutuwata?Ina ribar da za a samu daga zuwana kabari?Ko matattu suna iya yabonka?Za su iya shelar madawwamin alherinka?
10 Ka ji ni, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai!Ka taimake ni, ya Ubangiji!