1 Mai farin ciki ne wanda yake kula da matalauta,Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake shan wahala.
2 Ubangiji zai kiyaye shi, yă keɓe ransa.Ubangiji zai sa yă ji daɗi a ƙasar,Ba zai bar shi a hannun magabtansa ba.
3 Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake ciwoYa mayar masa da lafiyarsa.
4 Na ce, “Na yi maka zunubi, ya Ubangiji,Ka yi mini jinƙai ka warkar da ni!”
5 Magabtana suna mugayen maganganu a kaina,Suna cewa, “Yaushe ne zai mutu a manta da shi?”
6 Masu zuwa su gaishe ni ba da zuciya ɗaya suke zuwa ba,Sukan tattara duk mugun labari a kainaSa'an nan su je su yi ta bazawa ko'ina.