2 Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo,Mai kyan gani ne na Allah,Birnin babban Sarki.Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!
3 Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa,A kagarar birnin.
4 Sarakuna suka tattaru,Suka zo Dutsen Sihiyona,
5 Da suka gan shi sai suka yi mamaki,Suka tsorata suka gudu.
6 Tsoro ya kama su suka razana,Kamar mace wadda take gab da haihuwa.
7 Allah yakan hallaka manyan jiragen ruwa da iskar gabas.
8 Mun ji labarin waɗannan al'amura,Yanzu kuwa mun gan suA birnin Allahnmu, Mai Runduna,Zai kiyaye birnin lafiya har abada.