6 Adalai za su ga wannan, su ji tsoro,Za su yi maka dariya, su ce,
7 “Duba, ga mutumin da bai dogara ga AllahDon ya sami zaman lafiyarsa ba.A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa.Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”
8 Amma ni, kamar itacen zaitun nake, wanda yake girma kusa da Haikalin Allah,Ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa har abada abadin.
9 Zan gode maka, ya Ubangiji,Saboda abin da ka aikata.Zan dogara gare ka,Sa'ad da nake sujada tare da jama'arka,Domin kai mai alheri ne.