3 Amma dukansu sun koma baya,Su duka mugaye ne,Ba wanda yake aikata abin da yake daidai,Babu ko ɗaya.
4 Allah ya ce, “Ashe, ba su sani ba?Ashe, mugayen nan jahilai ne?Ta wurin yi wa jama'ata fashi suke rayuwa,Ba sa yin addu'a gare ni.”
5 Amma sa'an nan za su firgita ƙwarai,Irin yadda ba su taɓa yi ba,Gama Allah ya warwatsa ƙasusuwan maƙiyanka.Ya kore su sarai, saboda ya ƙi su.
6 Dā ma ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona!Sa'ad da Allah ya sāke arzuta jama'arsa,Zuriyar Yakubu za ta yi farin ciki,Jama'ar Isra'ila kuwa za ta yi murna.