16 Amma ina kira ga Allah, yă taimake ni,Ubangiji kuwa zai cece ni.
17 Koke-kokena da nishe-nishenaSuna hawa zuwa gare shi da safe, da tsakar rana, da dad dare,Zai kuwa ji muryata.
18 Zai fisshe ni lafiyaDaga yaƙe-yaken da nakan yi da magabtana masu yawa.
19 Allah, shi wanda yake mulki tun fil azal,Zai ji ni, zai kore su.Ba abin da suka iya yi a kai,Domin ba su tsoron Allah.
20 Abokina na dā,Ya yi wa abokansa faɗa,Ya ta da alkawarinsa.
21 Kalmominsa sun fi mai taushi,Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa,Kalmominsa sun fi mai sulɓi,Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.
22 Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji,Zai kuwa taimake ka,Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.