5 Ka bayyana girmanka ya Allah, a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
6 Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni,Damuwa ta fi ƙarfina.Sun yi wushefe a kan hanyata,Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.
7 A shirye nake, ya Allah,Na shirya sosai!Zan raira waƙoƙi in yabe ka!
8 Ka farka, ya raina!Ku farka, molona da garayata!Zan sa rana ta farka!
9 Zan gode maka a cikin sauran al'umma, ya Ubangiji!Zan yabe ka a cikin jama'a!
10 Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har sammai,Amincinka kuma har sararin sammai.
11 Ka bayyana girmanka, ya Allah, a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!