14 Da maraice maƙiyana suka komo,Suna yaƙe haƙora kamar karnukan da suke yawo ko'ina a birni.
15 Suna kai da kawowa ko'ina neman abinci,In ba su sami abin da ya ishe su ba,Sukan yi gunaguni.
16 Amma zan raira waƙa a kan ikonka,Kowace safiya zan raira waƙa da ƙarfiGa zancen madawwamiyar ƙaunarka.Kai mafaka ne a gare ni,Wurin ɓuya a kwanakin wahala.
17 Zan yabe ka, mai tsarona,Allah ne mafakata,Allah wanda ya ƙaunace ni.