4 Ba domin na yi wani laifi ba, ya Ubangiji,Har da suka gaggauta gāba da ni.Kai da kanka ka gani, ya Allah na Isra'ila!Ka tashi ka taimake ni.
5 Ka tashi, ya Ubangiji, Allah Maɗaukaki, ka taimake ni,Ka tashi ka hukunta al'ummai,Kada ka yi wa waɗannan mugaye, maciya amana, jinƙai!
6 Da maraice suka komo,Suna yaƙe haƙora kamar karnukan da suke yawo ko'ina a birni.
7 Ji abin da suke fada!Harsunansu suna kama da takuba a bakinsu,Duk da haka suna ta tambaya, suna cewa, “Wa zai ji mu?”
8 Amma kai dariya kake yi musu, ya Ubangiji,Ka mai da al'ummai duka abin bandariya!
9 Mai tsarona, kai ne kake kiyaye ni,Kai ne mafakata, ya Allah.
10 Allahna wanda yake ƙaunata, zai zo gare ni,Zai sa in ga an kori magabtana.