10 Ka kwarara ruwa mai yawa a gonakin da aka nome,Ka jiƙe su da ruwa,Ka tausasa ƙasar da yayyafi,Ka sa ƙananan tsire-tsire su yi girma.
11 Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka!Inda ka tafi duka akwai wadata!
12 Makiyaya suna cike da tumaki masu ƙiba,Tuddai kuma suna cike da farin ciki.
13 Sauruka suna cike da tumaki,Kwaruruka suna cike da alkama,Suna sowa suna raira waƙa ta farin ciki!