11 Na sa tufafin makoki,Sai suka maishe ni abin dariya.
12 A tituna suna ta magana a kaina,Bugaggu da giya kuwa suna raira waƙa a kaina.
13 Amma ni, zan yi addu'a gare ka, ya Ubangiji,Ka amsa mini, ya Allah, a lokacin da ka zaɓa,Sabili da muhimmiyar ƙaunarka,Saboda kana cika alkawarinka na yin ceto.
14 Ka cece ni daga nutsewa cikin wannan laka,Ka kiyaye ni daga maƙiyana,Daga kuma wannan ruwa mai zurfi.
15 Kada ka bar ambaliyar ruwa ta rufe ni.Kada ka bar ni in mutu cikin zurfafa,Ko in nutse a cikin kabari.
16 Sabili da madawwamiyar ƙaunarka, ka amsa mini, ya Ubangiji,Ka juyo wurina, saboda juyayinka mai girma!
17 Kada ka ɓoye kanka daga bawanka,Ina shan babbar wahala, ka yi hanzari ka amsa mini!