7 Sabili da kai ne aka ci mutuncina,Kunya ta rufe ni.
8 Kamar baƙo nake ga 'yan'uwana,Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.
9 Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a HaikalinkaTana iza ni a ciki kamar wuta,Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.
10 Na ƙasƙantar da kaina ta wurin yin azumi,Jama'a kuwa suka ci mutuncina.
11 Na sa tufafin makoki,Sai suka maishe ni abin dariya.
12 A tituna suna ta magana a kaina,Bugaggu da giya kuwa suna raira waƙa a kaina.
13 Amma ni, zan yi addu'a gare ka, ya Ubangiji,Ka amsa mini, ya Allah, a lokacin da ka zaɓa,Sabili da muhimmiyar ƙaunarka,Saboda kana cika alkawarinka na yin ceto.