16 Zan tafi in yi yabon ikonka, ya Ubangiji Allah,Zan yi shelar adalcinka,Naka, kai kaɗai.
17 Kai ne ka koya mini, ya Allah, tun lokacin da nake yaro,Har wa yau kuwa ina ba da labarin ayyukanka masu banmamaki.
18 Yanzu da na tsufa, na kuma yi furfura,Kada ka rabu da ni, ya Allah!Ka kasance tare da ni sa'ad da nake shelar ikonka da ƙarfinka ga mutanen dukan zamanai masu zuwa.
19 Adalcinka, ya Allah, ya kai har sammai.Ka aikata manyan ayyuka,Ba waninka!
20 Ka aiko mini da wahala da azaba,Amma za ka mayar mini da ƙarfina,Za ka tashe ni daga kabari.
21 Za ka girmama ni har abada,Za ka sāke ta'azantar da ni.
22 Hakika zan yabe ka da garaya,Zan yabi amincinka, ya Allahna.Da garayata zan yi maka waƙoƙi,Ya Mai Tsarki na Isra'ila.