1 Ya Ubangiji, a koyaushe kai ne wurin zamanmu.
2 Kafin a kafa tuddai,Kafin kuma ka sa duniya ta kasance,Kai Allah ne, Madawwami.Ba ka da farko, ba ka da ƙarshe.
3 Kakan sa mutane su koma yadda suke,Su zama ƙura.
4 A gare ka shekara dubu, kamar kwana ɗaya ne,Kamar jiya ce wadda ta shige,Gajeruwa ce kamar sa'a guda ta dare.
5 Kakan kwashe mutane kamar yadda ambaliyar ruwa take yi,Kamar mafarki suke, ba su daɗewa.Kamar tsire-tsire suke waɗanda suke tsirowa da safe,
6 Su yi girma har su yi huda,Sa'an nan su yi yaushi su bushe da yamma.