3 Kakan sa mutane su koma yadda suke,Su zama ƙura.
4 A gare ka shekara dubu, kamar kwana ɗaya ne,Kamar jiya ce wadda ta shige,Gajeruwa ce kamar sa'a guda ta dare.
5 Kakan kwashe mutane kamar yadda ambaliyar ruwa take yi,Kamar mafarki suke, ba su daɗewa.Kamar tsire-tsire suke waɗanda suke tsirowa da safe,
6 Su yi girma har su yi huda,Sa'an nan su yi yaushi su bushe da yamma.
7 Mun halaka ta wurin fushinka,Mun razana saboda hasalarka.
8 Ka jera zunubanmu a gabanka,Zunubanmu na ɓoye kuwa,Ka sa su a inda za ka gan su.
9 Fushinka ya gajerta tsawon ranmu,Ranmu ya ƙare kamar ajiyar zuciya.