1 Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji,Gama ya aikata ayyuka masu banmamaki!Ta wurin ikonsa, da ƙarfinsa mai tsarki ya yi nasara.
2 Ubangiji ya bayyana cin nasararsa,Ya sanar da ikonsa na ceto ga sauran al'umma.
3 Ya cika alkawarinsa wanda ya yi wa jama'ar Isra'ila,Da tabbatacciyar ƙauna da aminci.Dukan mutane ko'ina sun ga nasarar Allahnmu!
4 Ku raira waƙa ta farin ciki ga Ubangiji.Dukanku waɗanda suke a duniya,Ku yabe shi da waƙoƙi, kuna ta da murya da ƙarfi,Saboda farin ciki!
5 Ku raira yabbai ga Ubangiji da garayu,Ku kaɗa garayu!