4 Ka tuna da ni sa'ad da za ka taimaki jama'arka, ya Ubangiji!Ka sa ni cikinsu, sa'ad da za ka cece su.
5 Ka yardar mini in ga wadatar jama'arka,In yi tarayya da jama'arka da farin cikinsu,In yi farin ciki tare da waɗanda suke murna ta fāriya domin su naka ne.
6 Mun yi zunubi yadda kakanninmu suka yi,Mugaye ne, mun aikata mugunta.
7 Kakanninmu a MasarBa su fahimci ayyukan Allah masu banmamaki ba,Sau da yawa sukan manta da irin ƙaunar da ya nuna musu,Suka tayar wa Mai Iko Dukka a Bahar Maliya.
8 Amma duk da haka ya cece su, kamar yadda ya alkawarta,Domin ya nuna ikonsa mai girma.
9 Ya tsauta wa Bahar Maliya, ta ƙafe,Har ya bi da jama'arsa su hayeKamar a bisa busasshiyar ƙasa.
10 Ya cece su daga maƙiyansu,Ya ƙwato su daga wurin abokan gābansu.