1 Kamar yadda kishimi yake marmarin ruwan sanyi daga rafi,Haka nake marmarinka, ya Allah.
2 Ina jin ƙishinka, ya Allah, ya Allah Mai Rai,Yaushe zan tafi in yi sujada a gabanka?
3 Dare da rana ina kuka,Hawayena kaɗai su ne abincina,A kowane lokaci maƙiyana suna ta tambayata,“Ina Allahnka?”
4 Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce,Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah,Ina bishe su a jere.Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa,Suna ta da murya, suna yabon Allah.
5 Me ya sa nake baƙin ciki haka?Me ya sa nake damuwa ƙwarai?Zan dogara ga Allah,Zan sāke yin yabonsa,Mai Cetona, Allahna.
6 Zuciyata ta karaiSaboda haka zan tuna da kaiA wajen Urdun, da kusa da Dutsen Harmon, da na Mizar,Zan tuna da kai.
7 Zurfafan tekuna suna kiran junansu,Matsirgar ruwa na Allah kuwa suna ta ruri!Igiyoyin ruwa na baƙin cikiSuka yi wa raina ambaliya.