3 A gare ka zan yi addu'a, ya Ubangiji,Da safe za ka ji muryata,Da hantsi zan yi addu'ata,In kuma jira amsa.
4 Kai ba Allah mai yarda da aikin kuskure ba ne,Ba ka yarda da mugunta a gabanka.
5 Ba ka jurewa da ganin mutane masu fāriya,Kana ƙin mugaye.
6 Kakan hallakar da duk maƙaryata,Kakan raina masu ta da hankali da masu ruɗi.
7 Amma ni, ina iya zuwa wurinka,Saboda ƙaunarka mai girma,In yi sujada a tsattsarkan Haikalinka,In kuma rusuna maka da bangirma.
8 Ina da abokan gāba da yawa, ya Ubangiji,Ka bi da ni in aikata nufinka,Ka kuma fayyace mini hanyarka domin in bi ta!
9 Abin da maƙiyana ke faɗa,Ba abin da za a yarda da shi ba ne,Su dai, so suke su hallakar kawai,Bakinsu kamar buɗaɗɗen kabari yake,Maganganunsu kuwa suna da taushi da kuma yaudara.