1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi jinƙai,Gama na zo gare ka neman tsira.Zan sami kāriya a ƙarƙashin fikafikanka,Sai dukan hatsari ya wuce.
2 Zan yi kira ga Allah, Maɗaukaki,Zan yi kira ga Allah, mai biyan dukan bukatata.
3 Daga sammai Allah zai amsa mini,Zai kori waɗanda suka tasar mini,Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa.
4 Raina yana tsakiyar zakoki,Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane.Haƙoransu kamar māsu da kibau suke,Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi.
5 Ka bayyana girmanka ya Allah, a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!
6 Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni,Damuwa ta fi ƙarfina.Sun yi wushefe a kan hanyata,Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.
7 A shirye nake, ya Allah,Na shirya sosai!Zan raira waƙoƙi in yabe ka!